Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sojojin da suka yi bore a Mali sun kafa gwamnatin rikon kwarya
2020-08-19 19:31:25        cri
A yau ne sojojin da suka yi bore a kasar Mali, suka sanar da kafa kwamitin da zai ceto al'ummar kasar (NSCP) wanda zai jagoranci mika mulki ta hanyar shirya babban zabe, bayan murabus din da shugaban kasar Ibrahim Boubacar Keita da kuma rusa gwamnati da majalisar dokokin kasar.

Haka kuma, kakakin sojojin ya sanar da jerin shawarwari da aka zartas Larabar nan, har zuwa wani lokaci, da suka hada da rufe iyakokin kasar ta sama da ta kasa, da kuma dokar hana fita daga karfe 9 na dare zuwa 5 na safe agogon wurin.

Jiya Talata da rana ne dai, sojoji a sansanin Soudiata Keita dake Kati suka yi bore, inda suka yi awon gaba da shugaba Ibrahim Boubacar Keita da firaministansa, suka kuma tsare a barikin soja dake Kati. Daga bisani ne kuma shugaba Keita ya fito ta kafar talabijin na kasar da yammacin jiya Talata, inda ya sanar da yin murabus tare da rusa gwamnati da majalisar dokokin kasar.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China