Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Shugabannin Afirka sun bukaci a hanzarta sakin shugaban Mali da ake tsare da shi
2020-08-21 20:47:39        cri
Shugabannin kasashen Afirka, sun yi Allah wadai da kakkausar murya kan juyin mulkin ranar Talata da wasu sojoji masu bore suka yi a kasar Mali, har ma suka tsare shugaba Ibrahim Boubacar Keita.

Shugaba da suka hada Uhuru Kenyatta na Kenya, da takwarorinsa na Afirka ta kudu da Jamhuriyar demokiradiyar Congo, da Rwanda, da Mozambique da sauransu, sun kuma bukaci da a hanzarta sakin Keita.

A wata sanarwar da shugabannin suka fitar a Nairobin kasar Kenya Jumma'ar nan, bayan wani taro da suka gudanar ta kafar bidiyo jiya da dare, sun yi kira da a gaggauta sakin manyan jami'an gwmamnatin sa, ciki har da Firaminista Boubou Cisse.

Kenyatta, ya kuma bukaci da a hanzarta warware rikicin kasar ta Mali cikin lumana bisa tsarin demokuradiyya, yayin da shugaban kasar Afirka ta kudu Cryril Ramaposa, ya yi kira da a gudanar da tattaunawa, don dawo da zaman lafiya da kwanciyar hanali a kasar dake yammacin Afirka.

Shi ma shugaba Felix Tshisekedi na Jamhuriyar demokiradiyar Congo (DR Congo) ya bukaci kasashen Afirka, da su cimma matsaya kan wannan batu, yana mai cewa, juyin mulkin "hadari ne ga tsarin demokuradiya a Afirka". (Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China