Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasashen duniya sun yi watsi da sabbin takunkuman da Amurka ke neman kakabawa Iran
2020-09-22 09:52:16        cri

Matakin da kasar Amurka ta sanar jiya Litinin, na sake kakabawa wasu hukumomi da daidaikun mutane dake goyon shirin nukiliyar kasar Iran takunkumi, ya gamu da rashin amincewar kasashen duniya.

Shugaba Donald Trump na Amurka dai, ya bayar da umarnin shugaba dake kakaba takunkumin hana fitar da kayayyaki kan sama da gomman hukumomi da daidaikun mutane, dake goyon bayan shirin nukiliyar Iran, da makamai masu linzami, da ma ayyuka da suka shafi makaman yau da kullum na kasar.

Da yake karin haske yayin wani taron manema labarai tare da wasu manyan jami'an Amurkar, sakataren harkokin wajen kasar Amurka Mike Pompeo, ya bayyana cewa, shugaba Nicolas Maduro na Venezuela, na daga wadanda Amurka take shirin kakabawa takunkumin, saboda alakarsa da mahukuntan Iran game da ayyukan Iran da suka shafi makamai.

Sauran sassan da takunkumin Amurkar zai shafa, sun hada da ma'aikatar tsaron Iran da tsare-tsare dakarun kasar, da kungiyar masana'antun tsaron kasar da darektanta, gami da daidaikun mutane, da hukumomi dake da alaka da hukumar makamashin nukiliyar kasar ta Iran.

Da yake mayar da martani, ministan harkokin wajen Iran, Mohammad Javad Zarif, ya yi Allah wadai da yunkurin Amurka na kakaba takunkumin, yana mai cewa, wannan ba wani sabon abu ba ne. ya ce Amurka dai tana son ganin ta kuntatawa Iran ta kowa ce hanya, ta yadda za ta musgunawa al'ummar mu, amma ba za ta yi nasara ba.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China