Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Jakadan Sin: Sanarwar Amurka ta kashin kanta game da maido da takunkumin MDD kan Iran haramtacce ne
2020-09-21 10:18:01        cri
Zhang Jun, zaunannen wakilin kasar Sin a MDD, a ranar Lahadi ya rubuta wasika ga shugaban kwamitin sulhun MDD, inda ya bayyana rashin amincewa da matakin da Amurka ta dauka na kashin kanta, inda ta sanar da maido da takunkumin MDD kan kasar Iran a ranar Asabar.

A cikin wasikar, Zhang yace, Amurka tayi gaban kanta ta fice daga hadaddiyar yarjejeniyar JCPOA a watan Mayun shekarar 2018, kuma a yanzu bata cikin masu ruwa da tsaki a yarjejeniyar JCPOA. Don haka, Amurka bata da hurumin neman bukatar kwamitin sulhun MDD ya maido da batun kakaba takunkumin Iran.

A martanin wasikar da Amurkar ta rubuta a ranar 20 ga watan Agusta, tun da farko mambobi 13 na kwamitin sulhun MDD sun rubuwa shugaban kwamitin inda suka yi bayani karara dake bayyana cewa duk wani mataki ko shawara da aka dauka a sanadin wasikar da Amurka ta rubuta haramtacce ne, kuma ba shi da wani tasiri a siyasance. Kana ra'ayin nasu ya samu karbuwa daga shugaban kwamitin sulhun.

Wakilin na Sin yace, kasarsa a shirye take wajen kokarin tabbatar da yarjejeniyar JCPOA da kuma mutunta kudirin kwamitin sulhun MDD, kuma zata yi iyakar bakin kokarinta wajen lalibo bakin zaren warware batun nukiliyar Iran ta hanyar matakan siyasa.(Ahmad)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China