Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Uganda ta kaddamar da hirin samar da hidimomin kudi ga 'yan gudun hijira
2020-03-18 11:53:35        cri

Kasar Uganda ta kaddamar da wani shiri na shekaru biyu wanda zai baiwa 'yan gudun hijirar kasar damar samun hidimomin kudi don inganta rayuwarsu.

Juliet Tumuzoire, shugabar hukumar zurfafa harkokin kudade, wata hukuma ce mai zaman kanta ta kasar Uganda, tace ana fata bayan kammala shekaru biyu ana sa ran sama da 'yan gudun hijira 200,000 ne za su samu hidimomin kudi da za su inganta rayuwarsu.

Tumuzoire tace taken shirin shi ne "Samar da damar kudade ga 'yan gudun hijira," ana fatan shirin zai amfanawa 'yan gudun hijira na yankuna biyar cikin yankunan 28 na kasar.

Uganda ce kasar dake da mafiya yawan 'yan gudun hijira a nahiyar Afrika wanda yawansu ya kai miliyan 1.4, a bisa kididdigar MDD. A cewar gwamnatin kasar, kashi 13 bisa 100 na 'yan gudun hijirar kasar ne ke iya samun hidimomin kudi sabanin kashi 78 bisa 100 na 'yan kasar ta Uganda. (Ahmad)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China