Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Shugaban majalisar rikon kwaryar Sudan ya kama hanyar zuwa UAE
2020-09-21 10:40:40        cri
A jiya ne, shugaban majalisar rikon kwaryar kasar Sudan Abdel Fattah al-Burhan, ya tashi zuwa hadaddiyar daular Larabawa (UAE), don gudanar da wata ziyarar aiki ta kwanaki biyu kan batutuwan kasar dake da nasaba da shiyyar.

Wata sanarwa da majalisar ta fitar, ta bayyana cewa yayin ziyarar, Al-Burhan zai tattauna da shugabannin kasar, yayin da manyan ministocin dake rufa masa baya, za su tattauna da wata tawagar gwamnatin Amurka da tuni ta isa kasar, a kokarin da ake na ganin Amurkar ta cire kasar ta Sudan daga jerin sunayen kasashen dake taimakawa ayyukan ta'addanci, da taimakawa gwamnatin rikon kwaryar kasar, da kuma soke mata basussukan da Amurkar ke binta.

Tun bayan cire tsohon shugaban kasar Sudan Omar al-Bashir daga mukaminsa a watan Afrilun shekarar 2019, tankiya tsakanin Khartoum da Washington ta kara tsananta, duk da wadannan batutuwa.

Tun a shekarar 1997 ne dai, Amurka ta fara kakabawa Sudan takunkumin tattalin arziki, aka kuma sanya ta cikin jerin kasashen dake daukar nauyin ayyukan ta'addanci tun a shekarar 1993.

Sai dai kuma, a shekarar 2017, Amurka ta yanke shawarar janye takunkumin da ta kakabawa kasar ta Sudan, amma kuma ba ta cire ta daga cikin jerin kasashen dake daukar nauyin ayyukan ta'addanci ba.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China