Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Rukunin sojojin kiyaye zaman lafiya na kasar Sin a Sudan ta kudu sun kammala aikin ba da kariya sau 10
2020-09-12 16:40:38        cri

Rukunin sojojin kiyaye zaman lafiya da kasar Sin ta tura zuwa Sudan ta kudu a karo na 6 sun kammala aikin da tawagar musamman ta MDD dake Sudan ta kudu ta danka masa na ba da kariya , da haka rukunin ya kammala makamancin wannan aiki har sau 10.

An ce, aiki a wannan karo ya shafi hanya mai tsawon kilomita fiye da 170, sojojin sun ratsa gadoji masu hadari da tasoshin bincike tare kuma da yin kandagarkin cutar Covid-19 yadda ya kamata.

Bayan sun koma sansaninsu lami lafiya, nan da nan ma'aikatan jiyya sun dauki matakin kashe kwayoyin cuta kan sojoji masu ba da kariya da motoci da kuma na'urori, tare kuma da killace masu shiga aikin. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China