2020-09-15 10:59:11 cri |
Ofishin shirin ayyukan jin kai na MDDr OCHA ya sanar da cewa, sama da gidaje 71,000 ne suka rushe, yayin da wasu karin gidajen 72,000 suka lalace, sannan sama da dabbobi 3,300 ambaliyar ruwan ta kashe.
Ofishin na OCHA ya ce, gwamnatin kasar, da hukumomin MDD, da kungiyoyi masu zaman kansu sun kai dauki da tallafin kayan abinci da na kiwon lafiya da sauransu ga mutane kimanin 200,000.
Hukumar dake kula da hasashen yanayi ta fitar da wani gargadi na yiwuwar samun mamakon ruwan sama da ambaliyar ruwa har zuwa ranar Talata, ko da yake, tashoshin dake sanya ido kan tekun Blue Nile sun samu raguwar ruwan tekun da mataki milimita 3 a karshen makon da ya gabata. (Ahmad)
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China