Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sudan ta bukaci a yi tattaunawa kan batun dam din Habasha tsakanin shugabannin kasashe
2020-08-30 16:35:10        cri

A ranar Asabar kasar Sudan ta bukaci a daga matsayin tattaunawa kan batun madatsar ruwa ta Habasha wato GERD a kogin Nile, daga taron ministoci zuwa taron shugabannin kasashen.

Ministan noman rani da albarkatun ruwa na kasar Sudan, Yasir Abbas, ya bayyana a taron manema labaru a Khartoum cewa, tilas ne a daga matsayin tattaunawar daga matakin ta ministoci zuwa ta shugabannin kasashen uku ta hanyar kungiyar tarayyar Afrika, domin a samu goyon bayan siyasa.

Abbas ya kara da cewa, ci gaba da yin tattaunawar bisa tsarin da ake yi a halin yanzu ba zai zama mai inganci ba, ya jaddada aniyar Sudan ta shiga tattaunawar a kowane lokaci kuma a kowane waje.

Ya ci gaba da cewa, batun cimma matsaya kan yarjejeniyar madatsar ruwa a kogin Nile yana bukatar shugabannin kasashen uku su tsai da kudurinsu.

A ranar Juma'a, kasashen Sudan, Masar, da Habasha suka kammala sabon zagayen tattaunawar da suka gudanar ba tare da cimma matsaya ba kan batun tsara daftarin yarjejeniyar madatsar ruwan ta GERD wanda ya kamata a gabatarwa kungiyar AU daftarin a ranar Juma'a. (Ahmad)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China