Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sudan na tunkarar zanga-zangar adawa da sauya dokokin kasar ta hanyar tsaurara tsaro a babban birnin kasar
2020-07-17 12:57:59        cri

Hukumomin tsaro a Sudan, sun rufe dukkan gadojin dake kaiwa babban birnin Khartoum, yayin da kungiyoyin musulmai ke ci gaba da kira da zanga-zangar adawa da gyara wasu dokokin kasar.

Wata sanarwar da hukumomin suka fitar, ta ce kwamitin tabbatar da tsaro na Khartoum, ya sanar da rufe dukkan gadojin birnin daga karfe 6 na yammacin jiya Alhamis har zuwa karshen yau Jumma'a, tana mai bukatar mazauna su bada hadin kai, su kuma kaucewa ayyukan da za su kai su ga tsallake gadojin a wancan lokaci da aka kayyade.

A makon da ya gabata ne, gwamnatin riko na kasar ta amince da gyara wasu dokoki, lamarin da ya janyo ce-ce-ku-ce.

Gwamnatin ta soke dokar hukuncin kisa ga wanda ya yi ridda, inda ta musanya shi da daurin shekaru 10 a gidan yari ga duk wanda ya alakanta wani musulmi da sunan kafiri ko ya zargi wani musulmi da yin ridda.

Bisa daukar wadannan gyare-gyare a matsayin keta dokokin shari'ar musulunci, musulmai da dama a kasar na kira da yin zanga-zanga, wanda aka tsara a yau Jumma'a. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China