Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sabuwar cinikayyar ba da hidima ta samar da sabbin damammakin raya cinikayyar "Ziri daya da hanya daya"
2020-09-08 14:12:19        cri

Yanzu, ana gudanar da bikin baje kolin cinikayyar ba da hidima na kasa da kasa na kasar Sin (CIFTIS) na shekarar 2020 a birnin Beijing. Bana shekaru 7 ke nan da kaddamar da shawarar "Ziri daya da hanya daya", mahalarta bikin sun mai da hankali kwarai kan harkokin bunkasuwa da sauye-sauyen da aka samu a tsarin cinikayyar ba da hidima na kasar Sin da kasashen dake kan hanyar "ziri daya da hanya daya".

Karin bayani daga Maryam Yang…

"Wannan ita ce barasar inabi ta kasar Georgia, muna da fasahar sarrafa barasar inabi ta musamman, muna amfani da gwangwanayen yumbu, barasar inabi da muka sarrafa tana da dandano na musamman."

A yankuna nune-nunan bikin CIFTIS na shekarar 2020, wani jami'in ofishin jakadancin kasar Georgia dake kasar Sin ya yi bayani game da barasar inabi na kasarsa, ya kuma yi maraba ga al'ummomin Sin da su kai ziyara kasar Georgia bayan wannan annoba, domin yawon shakatawa da sada zumunta a tsakaninsu da al'ummomin kasar Georgia.

A 'yan shekarun nan, cinikayyar ba da hidima tsakanin kasar Sin da kasashen dake kan hanyar "ziri daya da hanya daya" tana bunkasa cikin sauri. Amma, barkewar annobar cutar numfashi ta COVID-19 ta haddasa babbar asara a fannin cinikayyar ba da hidima, kamar sana'o'in yawon shakatawa da na zirga-zirga da sauransu.

A don haka, a yayin bikin CIFTIS na bana, ana mai da hankali kwarai kan yadda za a farfado da sana'o'in ba da hidima. Wasu kamfanonin yawon shakatawa na kasashen dake kan hanyar "ziri daya da hanya daya" sun halarci bikin domin farfado da ayyukansu. Mataimakiyar shugaban kamfanin yawon shakatawa na Sentosa na kasar Singapore Wang Jing ta bayyana cewa, damar da dukkanin kamfanoni suka samu ta halartar wannan biki tana da kyau sosai. Tana mai cewa, "Sana'ar yawon shakatawa ta kasar Sin tana cikin yanayi mai kyau, sakamakon nasarar da kasar Sin ta samu wajen dakile yaduwar cutar numfashi ta COVID-19, lamarin da ya samar da damammaki masu kyau ga bunkasuwar harkokin yawon shakatawa a kasar Sin, farfadowar yawon shakatawa a tsakanin larduna daban daban na kasar ya karfafa mana gwiwa sosai."

A lokacin da muke yaki da cutar COVID-19, muna kuma dukufa wajen habaka sabbin fannonin hadin gwiwar cinikayyar ba da hidima a tsakanin kasar Sin da kasashen dake kan hanyar "ziri daya da hanya daya".

Abin da muka saurara shi ne, bayanin da jami'in wata makarantar kasar Malaysia ya gabatar game da harkokin ba da ilmi na makarantar, ta kafar bidiyon a yayin bikin CIFTIS.

A yayin wannan annoba, an fito da sabon tsarin cinikayyar ba da hidima, wanda yake da makoma mai haske. Kamar ba da ilmi ta kafar bidiyo, yin kasuwanci tsakanin kasa da kasa ta yanar gizo, gudanar da ayyuka daga gida, da kuma biyan kudi ta yanar gizo da sauransu, lalle an cimma nasarori masu gamsarwa kan wadannan ayyuka.

A 'yan shekarun nan, cinikayya ta yanar gizo ta bunkasa matuka a kasar Sin. A shekarar 2019, darajar cinikayyar shigi da fice ta yanar gizo ya kai dallar Amurka biliyan 203.6 a kasar Sin, adadin da ya kai 26% na darajar cinikayyar ba da hidima, wanda ya karu da 6.7% idan aka kwatanta da na shekarar 2018. Lamarin da ya sa, wasu kasashen Turai suka gano sabbin damammakin raya hadin gwiwar dake tsakaninsu da kasar Sin, ta yadda za su cimma karin moriya. Mataimakin shugaban kungiyar 'yan kasuwa dake kasashen mambobin kungiyar EU ta kasar Sin Ma Xiaoli ya bayyana cewa, "Wasu gwamnatocin kasashen Turai sun halarci cinikayya ta yanar gizo cikin himma da kwazo, kuma ana habaka sabbin damammaki a fannoni da dama, domin mun san cewa, cinikayya ta yanar gizo ta samar mana da sabbin damammaki, ta yadda za mu shiga sabbin kasuwanni. kasashen Turai na ganin cewa, kasuwannin kasar Sin suna da muhimmanci matuka."

Su ma mahalarta bikin CIFTIS na kasar Sin da na kasashen ketare suna ganin cewa, bunkasuwar cinikayya ta yanar gizo ta kasar Sin ta ba da gudummawa wajen kyautata tsohon tsarin cinikayyar ba da hidima, da kuma inganta cinikayyar hajoji da harkokin zuba jari, ta yadda za a ci gaba da gina shawarar "ziri daya da hanya daya" cikin hadin gwiwa. (Maryam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China