Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Wang Yi: Ayyukan shawarar "ziri daya da hanya daya" na ci gaba da bunkasa duk da kalubalen da duniya ke fuskanta
2020-06-18 23:39:20        cri

A yau Alhamis, memban majalisar gudanarwa, kana ministan harkokin wajen kasar Sin, Wang Yi ya jagoranci babban taron hadin-gwiwar kasa da kasa kan shawarar "ziri daya da hanya daya" da aka shirya ta kafar bidiyo a Beijing.

Wang ya ce, duk da cewa duniya na fuskantar wasu matsaloli, ciki har da yaduwar annobar COVID-19, da tawayar tattalin arziki, amma hadin gwiwar kasa da kasa bisa shawarar "ziri daya da hanya daya" na ci gaba da bunkasa, har ma ana samun wasu sabon ci gaba.

Na farko, ana kara samun wasu kasashe a cikin shawarar. A shekarar da ta wuce, an daddale wasu sabbin yarjeniyoyi 29 tsakanin gwamnatocin kasa da kasa, abun da ya kai ga jimillar yarjeniyoyin zuwa dari biyu.

Na biyu, ana kara yin hadin-gwiwa a fannin tattalin arziki da kasuwanci. A bara, jimillar kudin cinikin da aka yi tsakanin kasar Sin da kasashen da suka shiga shawarar "ziri daya da hanya daya" ta zarce dala triliyan 1.3, adadin da ya karu da kaso 6 bisa dari.

Na uku, ana kara yin mu'amala da tuntubar juna tsakanin kasa da kasa, al'amarin da ya taimaka sosai ga bunkasuwar tattalin arziki da zamantakewar al'umma.

Wang Yi ya kara da cewa, ya kamata hadin-gwiwar da ake yi bisa shawarar "ziri daya da hanya daya" ya taimaka wajen dunkulewar duniya baki daya, da gudanar da kasuwanci cikin 'yanci, da kuma kyautata tafiyar da harkokin duniya.

A waje guda kuma, Wang ya jaddada cewa, a lokacin da duniya ke fuskantar barazanar yaduwar COVID-19, kasashen da suke cikin shawarar "ziri daya da hanya daya" sun baiwa kasar Sin babban goyon-baya, a nata bangare ita ma kasar Sin ta samar da tallafin yaki da cutar ga aminan da suke hadin-gwiwa 122, da tura tawagogin likitoci zuwa kasashe 25, don taimaka musu yakar wannan annoba.

Wang Yi ya kuma ce, yaki da annobar gami da farfado da tattalin arziki shi ne muhimmin aikin dake gaban kowace kasa a halin yanzu, kuma kasar Sin na son inganta mu'amala tare da kasashen dake cikin shawarar "ziri daya da hanya daya", da samar musu da goyon-baya a manyan fannoni biyar.

A cewar Wang, makasudin shirya irin wannan taro shi ne, domin kasar Sin na son fadada hadin-gwiwa da aminan huldarta, da karfafa imanin raya shawarar "ziri daya da hanya daya" da samun nasarar dakile annobar COVID-19.(Murtala Zhang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China