2019-11-27 11:14:17 cri |
Masanan sun ce, kasar Sin ta riga ta kulla yarjeniyoyin hadin gwiwa guda 197, da kasashe guda 137, da kungiyoyin kasa da kasa guda 30, bisa shawarar "ziri daya da hanya daya". Matakin da ta ba da taimako ga kasashen da abun ya shafa, wajen karfafa aikin raya muhimman ababen more rayuwa, da raya cinikayyar hajoji da ta hidima, da inganta aikin zuba jari, da samar da guraben aikin yi, ta yadda za a ba da gudummawa ga kasashen wajen kawar da talauci, da kyautata zaman rayuwar al'umma, da kuma inganta musayar al'adu.
Haka kuma sun ce, cikin gajeren lokaci, kasar Sin ta cimma nasarar raya muhimman ababen more rayuwa a yankuna da yawa, ta kuma sami fasahohi masu kyau, wadanda kasashe masu tasowa za su iya koyi daga gare su. Sin na son inganta hadin gwiwa da sauran kasashe masu tasowa, domin raya makomar bil Adama ta bai daya. (Maryam)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China