Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin: Yanayin kandagarkin COVID-19 yana kyautatuwa a yankin Xinjiang
2020-08-28 19:46:33        cri

Yayin taron ganawa da manema labaran da aka saba yi yau, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Zhao Lijian ya bayyana cewa, a halin yanzu, yanayin kandagarkin annobar cutar numfashi ta COVID-19 a yankin Xinjiang yana ci gaba da kyautatuwa.

Jami'in ya kara da cewa, tun bayan da annobar ta barke a wasu sassan yankin a watan Yulin bana, nan take hukumomin da abin ya shafa na gwamnatin yankin, suka dukufa wajen aiwatar da manufar mayar da rayukan al'ummun yankin kan gaba, suka dauki matakai a jere domin hana yaduwar annobar, tare kuma da tabbatar da tsaron rayuka da lafiyar jikin al'ummun yankin.

A sa'i daya kuma, sun yi iyakacin kokari, wajen jinyar masu dauke da cutar, kuma matakan da suka dauka sun samu amincewa matuka daga al'ummun yankin, ta yadda yanzu haka yanayin kandagarkin cutar ke kara kyautatuwa a kai a kai a yankin na Xinjiang.(Jamila)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China