Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Hajojin da aka yi sufurin su ta tashar layin dogo kan iyakar Xinjiang sun haura miliyan 25
2020-08-17 10:46:07        cri

Hukumar kwastam mai aiki a tashar layin dogo ta Alataw Pass, dake jihar Xinjiang a arewa maso yammacin kasar Sin, ta ce adadin hajojin da aka yi sufurin su ta layin dogon yankin ya kai sama da miliyan 25, wadanda kuma darajar su ta haura dala miliyan 80, tun bayan bude hada hadar cinikayya ta yanar gizo, da safarar kayayyaki zuwa kasashen ketare ta tashar a watan Janairun bana.

A cewar jami'in kwastam dake aiki a tashar ta Alataw Pass Mr. Yang Qian, hada hadar sufurin hajoji tsakanin Sin da Turai ta jiragen kasa ta tashar Alataw Pass ta samu bunkasa a bana, inda a yanzu haka jiragen kasan dakon hajoji dake bin hanyoyi 15 ke bin wannan tasha.

Rahotanni sun nuna cewa, an yi jigilar kayayyakin wasan yara, da kayan daki na katako, da tufafi, da sauran kayayyakin bukatu na yau da kullum, ta hanyar cinikayya ta yanar gizo zuwa kasashe Belgium, da Netherlands, da Jamus da sauran kasashen tarayyar Turai ta wannan tasha.

Mr. Yang ya ce cinikayyar yanar gizo tsakanin kasashen ketare, sabon salo ne na cinikayyar waje, wanda ya samar da tallafi wajen habaka tattalin arzikin gidan kasashe, tare da inganta cudanyar tattalin arziki. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China