Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Urumqi: za a kara yin gwajin COVID-19 ga wadanda suka taba kamuwa da cutar
2020-08-27 11:28:31        cri
Kakakin jihar Xinjiang mai cin gashin kanta ta kasar Sin Wang Wulong ya sanar da halin da jihar ke ciki na tinkarar annobar COVID-19 a jiya Laraba, inda ya bayyana cewa, a kokarin tabbatar da lafiyar jama'ar kabilu daban daban dake birnin Urumqi, hedkwatar jihar, da ma tsaronsu, tun daga wannan rana, za a kara yin binciken kwayar cutar ga wasu al'ummomin da a baya suka harbu da cutar, daga baya kuma za a kara daidaita manufofin dakile annobar, da farfado da tsarin komawa aiki da zaman rayuwa sannu a hankali.

Kakakin ya kara da cewa, bayan matakan da aka dauka, an samu kyautatuwar halin tinkarar annobar, matakin da ya kara inganta nasarar da aka samu a wannan fanni.

Bayanai na cewa, a ranar 25 ga wata, ba a samu sabbin wadanda suka kamu da cutar a jihar ta Xinjiang ba.

Hukumar ilmi ta jihar, ta sanar a jiya cewa, domin biyan bukatun ayyukan dakile annobar na jihar, za a jinkirta lokacin bude makarantun firamare da sakandare da kuma midil da ma gidajen renon yara, kana daga ranar 1 ga wata mai zuwa, za a fara koyarwa ta yanar gizo. (Bilkisu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China