Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Adadin mutanen da aka tabbatar sun kamu da COVID-19 a birnin Urumqi ya ragu
2020-08-02 16:24:58        cri

Darektar cibiyar kandagarkin cututtuka ta birnin Urumqi na jihar Xinjiang ta kasar Sin Rui Baoling ta bayyana jiya cewa, ya zuwa ranar 31 ga watan Yulin da ya gabata, adadin mutanen da aka tabbatar sun kamu da cutar numfashi ta COVID-19 da adadin mutanen da kwayar cutar COVID-19 ta harbe su amma ba su nuna alama ba sun ragu, amma birnin yana ci gaba da kasancewa a cikin yanayi mai tsanani, ya zama wajibi a ci gaba da daukan tsattsauran matakai domin shawo kan annobar tun da wuri.

Alkaluman sun nuna cewa, a ranar 31 ga watan Yulin, adadin sabbin mutanen da aka tabbatar sun kamu da cutar a birnin ya kai 31, adadin sabbin mutanen da suka kamu da cutar amma ba su nuna alama ba ya kai 8, kuma an sallame majinyata 7 daga asibiti bayan sun warke, kana mutanen da suka kamu da cutar amma ba su nuna alama ba guda 7 sun koma gida daga wurin da aka kebe domin binciken lafiyarsu.

Ya zuwa tsakar daren 31 ga watan Yulin, gaba daya adadin masu cutar dake kwance a asibiti a jihar Xinjiang ya kai 547, a cikinsu, masu cutar 544 suna birnin Urumqi, kana mutane 14540 suna wuraren da aka kebe domin binciken lafiyarsu.(Jamila)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China