Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An sallami mutane 47 bayan warkewa daga COVID-19 a babban yankin kasar Sin
2020-08-21 10:01:04        cri

Hukumar kiwon lafiya ta kasar Sin, ta tabbatar da warkewar karin mutane 47 daga cutar numfashi ta COVID-19, aka kuma sallame su daga asibiti a ranar Alhamis.

Hukumar wadda ta fitar da sabbin alkaluma a Juma'ar nan, ta ce har yanzu akwai mutane 491 dake jinyar wannan cuta, ciki hadda mutane 20 dake cikin mawuyacin hali.

Bisa jimilla, ya zuwa jiya Alhamis, adadin masu fama da cutar da suka warke a babban yankin na kasar Sin ya kai mutane 79,792, cikin daukacin mutane 84,917 da suka harbu da cutar. Kaza lika mutane 4,634 sun rasa rayukan su bayan shan fama da wannan annoba. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China