Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Za a baje kolin alluran riga da sauran kayayyakin COVID-19 a bikin CFTCs
2020-08-24 11:42:27        cri

Jami'in hukumar lafiya ta birnin Beijing, Zheng Jinpu, ya shaidawa taron manema labarai cewa, an gayyaci kamfanoni da masana'antu 105 wadanda suka fito daga kasashe ko yankuna 8, za su halarci bikin baje kolin hidimomi da harkokin cinikayya na kasar Sin na kasa da kasa dake da taken "Lafiya da tsaro ga kowa" da za a shirya a watan Satumba mai zuwa. Sannan kamfanoni 60 daga cikinsu za su tura wakilansu zuwa wajen bikin a zahiri.

Ya ce, a lokacin bikin baje kolin, za kuma a shirya wani taron tattaunawar batutuwan lafiyar al'umma, mai taken "hallara basirar duniya a fannin kandagarkjin annoba da yaki da barazanar cututtuka". An kuma shirya gayyatar masanan kasar Sin da na ketare kamar shehu malami Zhong Nanshan, dan cibiyar nazarin aikin Injinya ta kasar Sin, kan yadda za a gina al'umma mai koshin lafiyar bil-Adam da siffofin sabbin annoba. Haka kuma, za a tattauna darussan da Sin da kasashen duniya suka koya a fannin yaki da annobar.

A farkon watan Satumban wannan shekarar ce, ake sa ran shirya bikin baje kolin na CFTCs a birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin. (Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China