Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Li Keqiang zai halarci bikin rufe baje kolin lambunan shakatawa na shekarar 2019
2019-10-09 12:11:43        cri
A gun taron manema labaru da ofishin watsa labaru na majalisar gudanarwar kasar Sin ya shirya a jiya Talata game da ayyukan rufe bikin baje kolin lambunan shakatawa na kasa da kasa na shekarar 2019 da ake yi a nan birnin Beijing, daraktan kwamitin zartaswa na bikin baje kolin Gao Yan ta sanar da cewa, firaministan kasar Sin Li Keqiang zai halarci bikin rufe baje kolin a daren ranar 9 ga watan Oktoba, tare da gabatar da jawabi.

Shugabanni da manyan kusoshi da suka fito daga kasashen Pakistan, tsibiran Solomon, Cambodia, Kyrgyzstan, Azerbaijan da dai sauransu, da kuma wasu jami'ai na hukumar shirya baje koli ta duniya da kungiyar masu baje kolin lambunan shakatawa ta duniya, za su halarci bikin. Ban da wannan kuma, bikin zai samu halartar wadanda suka baje kayayyakinsu da 'yan kasuwa na duniya da shahararrun masana ilmin shuke-shuke da manema labaru na gida da na waje da kuma wakilai da suka fito daga ma'aikata da wurare daban daban na kasar Sin kimanin 900. Kafin rufe bikin kuma, Li Keqiang zai halarci dakin nune-nune na kasar Sin tare da shugabanni wasu kasashe. (Bilkisu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China