Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sama da masu yawon bude ido miliyan 2 sun ziyarci bikin baje kolin lambunan shakatawa na Beijing
2019-06-11 10:16:43        cri

Bisa alkaluman da hukumar kula da aikin shirya bikin baje kolin lambunan shakatawa na Beijing ta samu, ya zuwa daren ranar 9 ga wata, jimilar adadin masu yawon bude ido da suka ziyarci bikin tun bayan kaddamar da shi ya kai miliyan 2 da dubu 60, musamman ma a lokacin da ake murnar bikin Duanwu a karshen makon da ya gabata, adadin ya kai kusan dubu 138.

An samu labarin cewa, yayin bikin Duanwu, an shirya bukukuwan al'adu har sau 88 a cikin cibiyar daya bayan daya, wadanda suka jawo hankalin masu bude ido sama da dubu 62, ba kallon furanni masu kyan gani kadai ne ya kayatar da masu yawon bude ido ba, har ma da al'adun bikin Duanwu.

Jami'in hukumar shirya bikin baje kolin lambunan shakatawa na Beijing ya bayyana cewa, tun bayan kaddamar da bikin, wasu muhimman dakunan baje koli kamar su dakin kasar Sin, da dakin kasa da kasa, da dakin gwajin rayuwa, da dakin tsirrai da dakin wasan kwaikwayon Guirui sun fi samun karbuwa daga wajen masu yawon bude ido, ya zuwa daren ranar 9 ga wata, adadin masu yawon bude ido da suka ziyarci wadannan dakuna biyar ya kai miliyan 5 da dubu 260.(Jamila)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China