Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin ta warware matsalar karancin ruwan sha ga dukkanin masu fama da talauci
2020-08-22 16:20:38        cri
Jiya Jumma'a, ofishin yada labarai na gwamnatin kasar Sin ya kira taron manema labarai, inda wakilin ma'aikatar kula da albarkatun ruwa ya yi bayani kan aikin samar da isassun ruwan sha a dukkan yankunan karkarar kasar Sin. Ya ce, tun daga shekarar 2006, ya zuwa yanzu, kasar Sin ta daga matsayin aikin samar da isassun ruwa ga mutanen dake zama a kauyuka kimanin miliyan 256, inda ta warware matsalar karancin ruwan sha ga mutane masu fama da talauci kimanin miliyan 17.1. Bisa kididdigar da aka yi, a halin yanzu, an riga an warware matsalar karancin ruwan sha baki daya ga mutane masu fama da talauci a kasar Sin.

Kuma, ya zuwa karshen watan Yuli na bana, gaba daya, kasar Sin ta zuba jari na yuan biliyan 198.4 wajen gina ababen more rayuwa a fannin samar da ruwan sha a yankunan karkarar kasar, mutanen kauyuka sama da 80% suna amfani da ruwan famfo a halin yanzu, kuma, ingancin ruwan ya kyautata sosai, lamarin da ya sa, aka warware matsalar karancin ruwa baki daya. (Maryam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China