Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kamfanoni mallakar gwamnatin Sin suna inganta shirin taimakawa masu fama da talauci ta hanyar sayayya
2020-08-16 17:25:15        cri
Kwanan baya, wakilan kamfanoni mallakin gwamnatin kasar Sin guda 8 da suka hada da kamfanin man fetur na teku na kasar Sin, wato CNOOC, da kamfanin wutar lantarki na kasar Sin, da kamfanin makamashin kasar Sin da sauransu, sun shiga dakin watsa shirin sayar da kayayyaki ta bidiyo kai tsaye, domin gabatar wa masu sayayya kayayyaki masu nagarta da aka samu daga yankuna masu fama da talauci. Cikin sa'i'o biyar, gaba daya akwai mutane miliyan 3.87 da suka kalli shirin, inda aka sayar da amfanin gona daga yankuna masu fama da talauci da darajarsu ta kai yuan miliyan 11.29.

Shirin da aka yi ya kasance matakin taimakawa masu fama da talauci da kamfanonin mallakar gwamnati suka dauka. A bana, kwamitin sa ido da kula da dukiyoyi mallakar kasar Sin ya tsara shirin sa kaimi ga kamfanoni mallakar gwamnati da su taimakawa masu fama da talauci, domin ba da taimako ga masu fama da talauci wajen sayar da amfanin gona. Ya zuwa karshen watan Yuli kuma, kamfanonin mallakar gwmnatin kasar Sin sun riga sun saya da kuma sayar da amfanin gona na yankuna masu fama da talauci, da darajarsu ta kai yuan biliyan 3.17. (Maryam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China