Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Birnin Qingdao na lardin Shandong ya fidda sabon tsarin kula da tsofaffi
2020-08-20 21:47:36        cri
Ana fuskantar kalubalen kula tsofaffi a kasar Sin, saboda karuwar adadin tsofaffi a kasar. A birnin Qingdao na lardin Shandong na kasar Sin, an fitar da wani sabon tsarin kula da tsofaffi a fannin samun jinya domin inganta rayuwar tsofaffi.

Ma Shirui da uwargidansa suna zaune a gidan kula da tsofaffi na Zhongkang dake birnin Qingdao, sabo da diyarsu tana zama a ketare, domin kwantar da hankalin diyarsu, a watan Maris na shekarar 2019, sun kaura zuwa gidan kula da tsofaffi, inda za su samu kulawa yadda ya kamata.

Ma Shirui mai shekaru 89 yana fama da ciwon zuciya mai tsanani, uwargidansa Hu Yuling ta ce, a wannan wurin da suke zama, an hada harkokin kula da tsofaffi da ba da jinya tare, wannan shi ne, abin da ya fi janyo hankulansu, kuma, shi ne, suka kaura zuwa nan.

Cikin sama da shekara guda, Ma Shirui da uwargidansa Hu Yuling, suna sabawa da sabon wurin da suke zaune. Suna kuma jin dadin zamansu saboda yadda suke samun kulawa mai kyau, kuma, in akwai bukata, za su samu jinya daga likitoci kamar yadda suke fata. (Mai Fassarawa: Maryam Yang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China