Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Mai da alfanun jama'a gaban kome
2020-08-21 13:17:54        cri

Yayin rangadin da ya yi a lardin Anhui a kwanakin nan, shugaba Xi Jinping na kasar Sin ya kai ziyara da yin ta'aziyya ga iyalan mutanen da suka sadaukar da rayukansu domin yaki da ambaliyar ruwa, da duba yadda tattalin arzikin wuraren ke samun farfadowa, bayan da ruwa ya janye jikinsa.

 

Kafin haka, a watan Afrilun bana, Xi ya kai ziyara a lardin Shaanxi dake yammacin kasar Sin, inda ya duba yadda ake raya aikin gona a can, don taimakawa manoman wurin samun karin kudin shiga.

Ban da wannan kuma, a watan Yunin bana, Shugaba Xi ya ziyarci lardin Ningxia, inda ya yi rangadi don neman sanin yadda ake raya masana'antu a cikin kauyuka, don samarwa mutanen wurin damar inganta zaman rayuwa mai walwala.

Wadannan abubuwa da shugaban ya yi, na shaida wani ra'ayi mai muhimmanci na "mai da alfanun jama'a gaban kome" daga cikin manufofin mulki na kasar Sin. (Bello Wang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China