Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Ziyarar da Xi Jinping ya yi a gidajen wasu matalauta
2020-08-20 20:22:52        cri

Mista Wang Xianping, wani mutumin gundumar Pingli ta lardin Sha'anxi ne, ya dade yana shan wahalar zama a cikin yankin duwatsu, wurin da ke da wuyar gudanar da harkokinsa na yau da kullum, sakamakon rashin hanyoyi. Daga bisani an kwashe shi da iyalinsa aka mayar da su wani sabon gida, inda yake iya samun damar aiki a kusa da gidansa, lamarin da ya sa zaman rayuwarsa ya samu kyautatuwa sosai.

Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya ziyarci sabon gidansa a watan Afrilun bana, inda ya ce matakin sauyawa matalauta matsugunni zuwa wani sabon wuri mai kyakkyawan muhalli yana da muhammanci sosai, a kokarin da kasar Sin take yi na fidda matalauta daga kangin talauci.

Shugaba Xi Jinping na kasar Sin, ya ziyarci gidan wani tsoho mai suna Tan Dengzhou, a watan Afrilun shekarar 2019. Ganin yadda malam Tan da matarsa suke jin dadin zaman rayuwa ba tare da wata matsala a fannonin cin abinci, da ganin likita, da samun gidan zama ba, ya sa shugaban farin ciki matuka. Ya ce, idan wata manufa ta amfani jama'a, to, za mu tsaya kanta.

Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya ziyarci gidan malam Jeleoamu, wani manomi dan kabilar Yi ta kasar Sin, a watan Fabrairun shekarar 2018. Inda ya tattauna wasu dabarun da za a iya bi, don rage talauci a wannan kauye na Jeleoamu. Shugaba Xi ya gaya wa wani tsoho cewa, "Ya kamata ka yi amana da cewa, zaman rayuwarka zai kara kyau a nan gaba."

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China