Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Shugaban kasar Sin ya umarci sojoji da su kammala matakan dakile ambaliya da rage radadin bala'in da suka biyo baya
2020-08-20 20:42:23        cri
Shugaban kasar Sin Mr.Xi Jinping, ya umarci sojojin kasar, da su kara zage damtse wajen kammala ayyukan dakile ambaliya da rage radadin bala'i da suka biyo baya.

Xi, wanda ke ziyarar duba aikin dakile ambaliyar da rage radadin bala'i a lardin Anhui dake yankin gabashin kasar, ya ba da wannan umarni ne a yau Alhamis din, bayan ya saurari rahotanni daga sojoji kan yadda suke haduwa da mazauna yankin wajen shawo kan matsalar ambaliyar a sassan kasar.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China