Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Na'urar binciken duniyar Mars ta kasar Sin ta yi nisan km miliyan 8 daga doron duniya
2020-08-21 11:21:44        cri
Cibiyar binciken duniyar wata da sararin samaniya ta hukumar kula da sararin samaniyar kasar Sin, ta sanar a jiya cewa, na'urar binciken duniyar Mars ta kasar Sin, ta yi tafiyar sama da kilomita miliyan 8 daga doron duniyarmu, kuma tana aiki yadda ya kamata ba tare da wata matsala ba.

Zuwa karfe 11 da minti 20 na daren ranar Laraba, na'urar ta yi tafiyar kilomita miliyan 8.23 nesa da doron duniyarmu. Kana daga karfe 10 da minti 20 na dare a ranar, na'urorin dake jikinta da suka hada da ta auna karfin maganidisu da mai tsara taswira da kyamara, sun kammala bada tabbacin suna cikin ingantaccen yanayi. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China