Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kare Muradun Kasa Fiye Da Batun Rigakafin COVID-19 Na Barazana Ga Kokarin Da Kasashen Duniya Ke Yi Wajen Yaki Da Cutar
2020-07-14 14:24:20        cri

Ranar 12 ga wata, jaridar USA Today ta wallafa wani labari dake cewa, kasashen Amurka da Birtaniya da wasu kasashe ba su tsara da kuma aiwatar da tsare-tsaren duniya kan nazari da rarraba allurar rigakafin cutar annobar COVID-19 ba, inda suka kare muradun kasashensu kawai. Yadda suke kare muradun kasashensu fiye da batun rigakafin cutar yana barazana ga kokarin da kasashen duniya suke yi wajen yaki da cutar ta COVID-19. A don haka, ba za a samu lafiya a duniya ba, sai dai kowa ya yi kokarin samarwa kansa lafiya.

Haka zalika, jaridar Financial Times ta Birtaniya ta ba da labari a kwanan baya cewa, yanzu wasu kasashe, ciki had da Amurka da Birtaniya sun kare muradun kasa fiye da batun rigakafin cutar COVID-19. Inda suke goyon bayan nazarin allurar rigakafin cutar a kasashensu, yayin da suka bukaci a bai wa al'ummominsu allurar kafin sauran al'ummomin kasashen duniya.

Wasu masana lafiyar al'umma na duniya sun nuna damuwa cewa, yanzu babu wani tsari da aka bullo da shi game da yadda za a rarraba allurar tukuna, wanda ya samu amincewar sassa daban daban. David Fidler, babban manazarcin lafiyar al'ummar duniya a kwamitin kula da huldar jakadanci na Amurka ya bayyana ba tare da rufa-rufa ba cewa, da kyar a samu wani dan siyasa da zai ce, a fara bai wa kasashen Afirka da ke kudu da hamadar Sahara kaso 30 cikin 100 na allurar rigakafin cutar COVID-19. (Tasallah Yuan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China