Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Siyasantar da sanya makarin baki da hanci abun mamaki ne
2020-07-20 10:36:26        cri

Shugaban kwalejin nazarin kiwon lafiya na kasar Amurka wato NIH Francis Collins, ya bayyanawa 'yan jarida cewa, a yayin da ake tinkarar cutar COVID-19 a yanzu, abin mamaki ne a siyasantar da sanya makarin baki da hanci. A ganinsa babu wani zabi na daban game da sanya makarin baki da hanci.

Kafin hakan, shugaban kasar Amurka Donald Turmp ya bayyanawa 'yan jaridan kamfanin Fox News cewa, yana fatan jama'a za su samu 'yanci na zabar ko dai su sanya makarin baki da hanci ko a'a.

Doctor Collins ya kara da cewa, ko da hallitun dake rayuwa a wata duniya ta daban, idan suka zo duniyar nan za su yi mamaki game da siyasantar da makarin baki da hanci. Ya ce, bai taba tsammani za a hada ilmin kiwon lafiya da kowa ya sani da moriyar jam'iyyun siyasa ba. (Zainab)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China