Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Mutane sama da miliyan 5 sun harbu da cutar Covid-19 a Amurka
2020-08-11 12:29:50        cri

Ya zuwa ranar 9 ga wata, Amurka tana da yawan mutane sama da miliyan 5.05 da aka tabbatar sun kamu da cutar COVID-19, kana mutane 162,000 cutar ta kashe a kasar, kamar yadda alkaluman baya bayan nan game da cutar COVID-19 wanda jami'ar Johns Hopkins ta fitar ya nuna.

A cewar kafar yada labarai ta CNN, a halin yanzu Amurka ce take da kashi daya bisa hudu na yawan masu dauke da cutar COVID-19 a duniya baki daya, kuma ita ce ke da adadi mafi yawa na mutanen da cutar ta kashe a duniya.

Kwararrun masana kiwon lafiya da dama a Amurka sun bayyana cewa, duk da mummunar matsalar annobar da ake fama da ita a kasar ta Amurka, amma har yanzu gwamnati ba ta yin abinda ya dace waje dakile annobar. Hamshakin attajirin kasar Bill Gates ya fada a lokacin wata hira cewa, "babu wata kasa a duniya dake cikin rudani sama da Amurka. Gazawar da aka samu a farkon al'amari a Amurkar, gami da dalilai na siyasa, duk sun bayyana cewa, gwaje gwajen cutar sam ba su cikin tsarin ajandar kasar."

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China