Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Babban burin kasar Sin shi ne neman hanyoyin ci gaba tare da sauran kasashe masu tasowa
2020-08-13 16:39:09        cri

Ra'ayin mafi yawa daga masu fashin baki, game da harkokin raya tattalin arziki da kyautata zamantakewar al'umma, ya hadu kan muhimmancin samar da manyan ababen more rayuwa, a matsayin jigon ci gaban duk wata kasa, ko wata al'umma dake fatan kyautata rayuwar ta.

Tuni kasashen duniya suka dukufa wajen samar da ababen more rayuwa, da suka shafi harkokin inganta lafiya, sufuri, ilimi, hada hadar kudi, kasuwanci da dai sauran su. Suna kuma yin hadin gwiwa da kawaye da aminai wajen cimma wannan muhimmin buri.

Wannan bukata kuma, ita ce ta haifar da wajibcin neman rance, ko lamuni daga ko dai gwamnatocin kasashe masu wadata, ko kuma cibiyoyin kudi na kasa da kasa, gwargwadon bukata, ko kuma saukin samun rancen.

Da yawa daga kasashe masu tasowa, ciki hadda na nahiyar Afirka, sun lura da wajibcin neman rance daga wadancan irin sassa da muka ambata, domin ta haka ne kadai za su iya samar da manyan ababen more rayuwa da al'ummun suke bukata, wadanda kuma ke haifar da dama, ta fadadar hanyoyin raya tattalin arziki, da samar da guraben ayyukan yi.

To sai dai kuma a baya bayan nan, batun samar da rance, ko neman lamuni daga kasashe masu sukuni, na kara jan hankalin manazarta, duba da yadda a wasu lokuta, ake samun suka daga wasu sassa, dake ganin bashin da kasashe masu tasowa ke ci, tamkar wani tarko ne da zai kwacewa kasashen damar su ta cin gashin kai, ko ikonsu na mulkin kai.

Alal misali, a 'yan shekarun nan, wasu kasashen yammacin duniya sun rika sukar manufar kasar Sin, ta samar da rance mai rangwame ga kasashen nahiyar Afirka, suna masu bayyana matakin, da wani yunkuri na yiwa kasashen nahiyar sabon mulkin mallaka ko dana musu tarkon bashi. Zargin da kuma masana a fannin suka tabbatar da cewa, ba shi da tushe ko makama.

Idan ma muka kalli wannan zargi ta wata fuskar, za ku ga dalilin da ya sa irin wadancan kasashen yamma ke sukar kasar Sin, bai wuce batun takara da siyasar duniya ba. Wato dai irin wadannan kasashe na yamma, na kallo kasar Sin a matsayin abokiyar adawa, wadda ka iya kwace musu tasirin siyasa da suke da shi a nahiyar. Duk kuwa da cewa a lokuta da dama, Sin ta sha nanata cewa, ba ta da burin aiwatar da wata manufa ta mulkin mallaka, ko shan gaban wata kasa ta fuskar siyasa, a dukkanin inda ta kulla kawance da abokan hulda.

A 'yan kwanakin baya bayan nan, wani batu mai alaka da wannan shi ne, yadda wasu sassa na masu fashin baki, suka bullo da batun zargin cewa wai, an cusa wani sashen bayani dake iya ba da damar kwace ikon mulkin kai daga gwamnatin Najeriya, karkashin yarjejeniyar bashin da kasar ta karba, daga bankin shige da fice na kasar Sin, domin kammala kwangilar shekarar 2018 ta shimfida layukan dogo a Najeriyar.

To sai dai kuma, masu fashin baki, da masana tattalin arziki na kasashen biyu, sun bayyana kuskuren wannan zargi, suna masu cewa, ba yadda za a yi bashin da bankin na Sin ke bin Najeriya, ya haddasa kwace ikon mulkin kasar. Masana harkar dai sun tabbatar da cewa, makasudin sanya ayoyin yarjejeniyar karbar bashin shi ne, tabbatar da cewa, Najeriyar ta martaba yarjejeniyar da aka kulla, ta kuma biya bashin a kan lokaci kuma bisa tsarin da sassan biyu suka amincewa.

Idan kuwa muka nemi bahasin tasirin irin wadannan basussuka da Najeriya ke karba daga kasar Sin, a fili take cewa, Najeriya ta ci gajiyar maras iyaka daga gare su.

Kadan daga cikinsu kuwa, akwai aikin layin dogo da ya hade birnin Abuja, fadar mulkin kasar da jihar Kaduna wanda tuni aka kammala shi, aka kuma fara amfani da shi. Kaza lika akwai racen kudaden shimfida layin dogo tsakanin jihar Lagos dake kudu maso yammacin kasar, zuwa jihar Kano dake arewa maso yammacin kasar. Kari kan haka, Najeriyar na fatan samun wani rancen kudin, don shimfida layin dogo da zai hada birnin Port Harcourt na jihar Rivers dake kudu maso gabashin kasar, da birnin Maidugurin jihar Borno dake arewa maso gabashi.

Ke nan idan dai batu ake na ribar irin wadannan basussuka, ana iya cewa kwalliya ta riga ta biya kudin sabulu. Abun da ya rage kawai shi ne, mayar da hankali ga ci gaba da cin gajiya daga irin wadannan basussuka masu fa'ida bisa tsari, da kiyaye ka'idojin dake da alaka da su, tare da yin watsi da kalaman 'yan adawa, masu siyasantar da duk wata harka ta ci gaba. A kuma yi fatali da ra'ayin masu kokarin kawo baraka domin cimma bukatun kashin kai.

Muna dai ita gani a zahiri, daga hujjoji bayyanannu cewa, babban burin kasar Sin shi ne, neman bunkasa hanyoyin ci gaba tare da sauran kasashe masu tasowa, ba tare da gindaya wani sharadi da zai zamo tarnaki ga kasashe abokan huldar ta ba. (Saminu A.U)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China