Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Duwatsu Ba Za Su Iya Hana Samun Damar Fidda Kai Daga Talauci Ba
2020-08-09 18:38:57        cri

Gundumar Hezhang dake karkashin birnin Bijie na lardin Guizhou dake kudu maso yammacin kasar Sin tana wajen wani yanki mai duwatsu, inda a baya mutanen da suke zama a wurin su kan gamu da matsalar mu'amala tare da mutanen sauran wurare. Amma yanzu an gina hanyoyi da yawa a cikin duwatsu, abun da ya baiwa mutanen wurin damar yin ciniki don samun karin kudin shiga.

Yao Wenqian, wani manomi ne dake zama a kauyen Shui-Tang-Pu. Yanzu ya kan tuka mota don sayar da 'ya'yan itatuwa a kan hanya. Ya ce, bayan an gina wata hanyar mota mai inganci, ya samu sauki sosai yayin da yake jigila da sayar da kayayyaki.

"Dasa dankali zai sa a kawar da yunwa, yayin da dasa tufa zai sa a samu zaman rayuwa mai inganci"

A garin Yina, an fara gina wata babbar cibiyar samar da 'ya'yan tufa a shekarar 2015. A lokacin, wani manomi na wurin mai suna Peng Wencai ya yi sha'awar shiga aikin dasa tufa. Amma uwargidansa ba ta yarda ba, ta ce: "Dukkan kaka da kakaninmu suna dasa dankali ne da masara. Ko ba a samu girbin amfanin gona da yawa ba, za a iya samun isashen abinci. Yanzu kana son dasa tufa. Za a iya cin tufa a matsayin abincin yau da kullum ne?"

Don lallashin uwargidansa, Peng Wencai ya nuna mata kidayar da ya yi: bisa yin amfani da gonakinsu da fadinsu ya kai muraba'in mita 20,667, za a ba su Yuan 24,800 a kowace shekara. Kana yadda yake aiki a cibiyar dasa tufa zai ba shi damar samun albashin da ya kai a kalla Yuan 80 a kowace rana. Ban da haka, idan cibiyar ta samu riba, za ta raba kudi ga manoman.

Zuwa shekarar 2019, cibiyar ta fara samar da tufa, inda ta samu kudin da ya kai Yuan miliyan 61.5 bisa sayar da tufan. Wannan kudi ya sa dukkan mutane 17,232 dake kauyuka 7 morewa sosai, har ma an fidda wasu mutanen 2,952 daga kangin talauci. (Bello Wang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China