Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Wani kaya sai amale yadda gwamnatin Sin ta raya yankunan kasar ta hanayar layukan dogo na zamani
2020-08-10 17:09:43        cri

 

Lallai batun da masu azancin magana ke cewa himma ba ta rago ba ce ya tabbata, duba da irin namijin kokari da jajurcewar da mahukuntan kasar Sin suka yi wajen hada yankunan birane da na karkarar kasar ta hanyar giggina layukan dogo masu matsakaicin gudu da kuma masu saurin tafiya. Aikin gina layin dogo yana daga cikin muhimman kayayyakin more rayuwar jama'a wanda ke bukatar makudan kudade. Hakika fannin sufurin jiragen kasa wani muhimmin bangare ne dake saukaka harkokin zirga-zirga ga al'umma. Sai dai duk da dimbin makudan kudaden da aikin gina layin dogo ke lashewa, hakan ba kashe gwiwar hukumomin kasar Sin wajen aiwatar da wannnan muhimmin aiki ba. Bisa ga kididdigar da hukumar sufurin jiragen kasa ta kasar Sin ta fitar ya nuna cewa, ya zuwa karshen watan Yulin wannan shekarar, Sin tana da jimillar layin dogo da ya kai kilomita 141,400 wanda ya hade yankunan kasar daban daban, daga cikin wannan adadin da hukumar ta fitar, an ce akwai kilomita 36,000 na layin jirgin kasa mai saurin tafiya. Kasar ta zuba jarin kudin Sin da ya kai RMB yuan biliyan 67.1, kwatankwacin dala biliyan 9.67 a fannin sufurin jiragen kasa ya zuwa watan Yulin bana, wanda ya karu da kashi 3.6 bisa 100 idan an kwatanta da makamancin lokaci na shekarar da ta gabata, kamar yadda kamfanin kula da sufurin jiragen kasar ta Sin ya wallafa a shafinsa na intanet.

Adadin jarin da aka zuba a manya da matsakaitan ayyukan layin jirgin kasa a kasar Sin ya kai RMB yuan biliyan 49.9 a watan jiya, hakan ya nuna an samu karin kashi 11.3 bisa 100 na makamancin lokacin bara. A watanni bakwai na farko na wannan shekara, an gina sabbin layukan dogo da ya kai kilomita 1,310, kuma tuni sun riga sun fara aiki, wannan adadi ya hada da layin jirgin kasa mai saurin tafiya kilomita 733. Hakika aikin layukan dogon ya yi babban tasiri wajen kyautata harkokin sufuri a kasar Sin, da bunkasuwar tattalin arzikin kasar, da hada manyan birane da matsakaita na kasar, da kuma kyautata zaman rayuwar al'ummar Sinawa. (Ahmad Fagam CRI Hausa)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China