2020-07-17 20:40:37 cri |
Alkaluman tattalin arzikin kasar Sin a rubu'i na biyu na shekarar bana, da hukumar kididdigar kasar ta fitar a jiya Jumma'a sun jawo hankalin kasa da kasa, inda shahararren masani kan harkokin kasar Sin dan kasar Birtaniya Martin Jacques ke ganin cewa, karuwar tattalin arzikin kasar Sin a rubu'i na biyu na shekarar nan, na nuna karfin ci gaban tattalin arzikin kasar.
Martin Jacques ya kara da cewa, a rubu'in farko na bana, tattalin arzikin kasar Sin ya ragu da kaso 6.8 bisa dari, idan aka kwatanta da na makamancin lokaci a bara, amma a rubu'i na biyu, adadin ya karu da kaso 3.2 bisa dari, lamarin da ya bai wa al'ummun kasa da kasa matukar mamaki, kana ya nuna cewa, gwamnatin kasar Sin na da karfi matuka a fannin tafiyar da harkokin kasa.
Masanin ya kara da cewa, tun bayan rikicin hada-hadar kudi a fadin duniya a shekarar 2008, tattalin arzikin kasar Sin ya ci gaba da taimakawa sosai ga ci gaban tattalin arzikin duniya, kuma yanzu haka annobar COVID-19 tana bazuwa a sauran sassan duniya, yayin da tsarin tattalin arzikin duniya shi ma ya sauya, don haka kasar Sin za ta taka karin rawar gani, wajen ci gaban tattalin azikin duniya. (Jamila)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China