Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Za a kara samun wani wurin da za a iya koyon Sinanci a Najeriya
2020-08-09 20:31:04        cri

A ranar Alhamis da ta gabata, Madam Abdulrashim, sabuwar darektar cibiyar kula da albarkatun ilimi ta ERC dake Abuja, fadar mulkin kasar Najeriya, ta kulla yarjejeniyar hadin gwiwa tare da mista Li Xuda, mashawarcin jakadan kasar Sin dake Najeriya kan harkokin al'adu, inda suka tabbatar da cewa za a sake bude wani wurin koyar da yaren Sinanci na kasar Sin a cibiyar ERC, sa'an nan kasar Sin zata tura wasu malamai don su yi aikin koyarwa a cikin cibiyar. Ta wannan matakin, ana neman baiwa malamai na makarantun birnin Abuja damar samun horo a fannin yaren Sinanci.

Yayin da ake kulla wannan yarjejeniyar, Madam Abdulrashim ta ce tattalin arzikin kasar Sin na samun ci gaba cikin sauri, kana kasar tana kan gaba a duniya a fannonin kimiyya da fasaha, da kasuwanci, da al'adu, gami da fannin ilimi, ta yadda ta zama abin koyi ga kasashen dake nahiyar Afirka. Saboda haka, a cewarta, samun damar koyon Sinanci, don kara mu'amala da Sinawa, ta yadda za a iya koyon fasahohi na kasar Sin, yana da muhimmanci matuka ga mutanen Najeriya. Ta ce cibiyarta zata kara dora muhimmanci kan aikin koyar da yaren Sinanci, don taimakawa ayyukan rayan zaman al'umma da tattalin arziki na kasar Najeriya.

A nasa bangare, mista Li Xuda ya ce yayi amanna cewa bisa hadin gwiwar bangarorin Najeriya da Sin, aikin koyar da Sinanci a cibiyar ERC zai samar da sakamako mai kyau. (Bello Wang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China