Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
'Yar Nijeriya mai neman takarar shugabancin WTO ta ce za ta bada fifiko ga gyara tsarin warware rikici na kungiyar
2020-08-04 10:33:10        cri
'Yar Nijeriya mai neman takarar shugabancin hukumar kula da cinikayya ta duniya (WTO) wato Ngozi Okonjo-Iweala, ta ce idan aka zabe ta, za ta mayar da hankali kan gyara tsarin warware rikici na hukumar dake da mazauni a Geneva.

Cikin wata tattaunawa da ta yi a baya-bayan nan da kamfanin dillancin labarai na Xinhua, Ngozi Okonjo-Iweala dake takarar tare da wasu mutum 7, ta ce abubuwan da za ta ba fifiko idan aka zabe ta sun hada da; shiryawa taron ministocin kasashen hukumar karo na 12 da za a yi badi a Kazakhstan, da farfado da tsarin warware rikici da kuma gyara kundin ka'idojin hukumar.

Yanzu haka, tsarin warware rikici na hukumar ya yi rauni. Kamata ya yi a ce, kungiyar wadda ke zaman kotun kolin warware rikice-rikicen cinikayya, nada akalla alkalai 7, inda ake bukatar alkalai 3 a mataki mafi karanci domin ta yi aiki.

Sai dai, gwamnatin Amurka ta shafe sama da shekaru 2 tana hana sabbin nade-nade, inda jami'an kasar ke ikirarin kotun na wuce huruminta.

Ngozi Iweala ta ce za ta mayar da hankali ne wajen gyara tsarin na warware rikici, saboda shi ne kashin bayan hukumar.

Ta ce idan ka'idoji ne ke tafiyar da hukuma, dole ne a samu inda za a sulhunta, tana mai cewa, a don haka, farfado da tsarin warware rikici zai zama abun da za ta mayar da hankali kai. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China