Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Masanin Najeriya: Ya kamata kasashen yamma su daina katsalandan kan harkokin Hong Kong
2020-07-31 11:03:59        cri

Kwanan baya, shugaban cibiyar nazarin harkokin kasar Sin dake Najeriya Charles Ounaiju ya wallafa wani bayani a jaridar Blueprint ta Najeriya mai taken "Bai kamata kasashen yamma su ci gaba da yin katsalandan kan batun dokar tsaron kasa mai nasaba da yankin Hongkong na kasar Sin ba". Inda masanin ya fada cewa , wasu kasashen yammacin duniya ba su da gaskiya ko kadan, inda suke ta kokarin yada jita-jita game da dokar tsaron kasar Sin dake da nasaba da yankin Hong Kong. A cewar masanin, yadda kasar Sin ta kafa wannan doka, abu ne da ya dace, domin za ta taimaka sosai wajen samar da kwanciyar hankali a yankin Hong Kong, gami da tabbatar da tsaro a kasar Sin, a don haka, kamata ya yi kasashen duniya su yi maraba da goyon bayan wannan doka.

Bayanin ya ce, bayan kafa da aiwatar da dokar tsaron kasa mai nasaba da Hongkong, wasu kasashen yamma, da suka hada da Amurka da Burtaniya, da Australia, da Canada, suka fitar da wasu sanarwoyin dake jirkita abun gaskiyar wannan doka. Abin da ya nuna cewa, wadannan kasashe ba su da gaskiya ko kadan. Hadaddiyar sanarwar da Sin da Birtaniya suka kulla a shekarar 1984 ta tanadi cewa, yankin Hong Kong zai kasance karkashin jagorancin gwamnatin tsakiyar jamhuriyar Jama'ar kasar Sin kai tsaye. Saboda haka, yadda wasu kasashen yamma ke neman yin katsalandan cikin harkokin yankin Hongkong, ya zama tsoma baki ne cikin harkokin cikin gidan kasar Sin, kana wani mataki ne na mulkin mallaka da kwace iko. Maganar da wadannan kasashe suka yi wai Hong Kong wani wuri ne da ake bukatar daukar matakai don kare 'yancin jama'a ba ta da gaskiya. Domin a hakika dai, mazauna yankin ba su taba samun 'yanci ba, har sai sun koma karkashin kulawar kasar Sin. Harkokin Hong Kong harkokin cikin gidan kasar Sin ne, don haka sauran kasashe sam ba su da ikon tsoma baki a ciki. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China