2020-07-23 21:20:36 cri |
Yau Alhamis, a nan Beijing Wang Wenbin, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin ya sake bayyana ra'ayin kasar Sin kan yadda kasar Amurka ta bukaci kasar Sin ta rufe karamin ofishin jakadancin Sin dake birnin Houston na Amurka. Ya kuma musunta labaru marasa gaskiya da Amurka ta baza.
Kakakin ya yi nuni da cewa, abun da Amurka ta yi ya saba wa dokokin kasa da kasa da kuma manyan ka'idojin raya hulda a tsakanin kasa da kasa, da ma yarjejeniyar da kasashen biyu suka cimma kan kafa karamin ofishin jakadanci. Amurka na neman illata huldar da ke tsakaninta da Sin, tare da rushe gadar zumunci a tsakanin al'ummun kasashen biyu. (Tasallah Yuan)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China