Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin za ta mayar da martani dangane da yadda Amurka ta bukaci Sin ta rufe karamin ofishin jakadancinta dake Houston
2020-07-22 20:44:33        cri

Wang Wenbin, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin ya bayyana yau Laraba a nan Beijing cewa, a jiya Talata 21 ga wata, kasar Amurka ta bukaci kasar Sin ta rufe karamin ofishin jakadancinta dake birnin Houston na Amurka ba zato ba tsammani. Amurka ta dauki wannan mataki ne domin ta da tsokana ta fuskar siyasa. Abun da ta yi ya saba wa dokokin kasa da kasa da kuma manyan ka'idojin raya hulda a tsakanin kasa da kasa, da ma yarjejeniyar da kasashen biyu suka cimma kan kafa karamin ofishin jakadanci. Amurka na neman illata huldar da ke tsakaninta da Sin ba tare da wani dalili ba. A don haka, kasar Sin ta yi tir da babbar murya kan wannan lamarin. Ta kuma bukaci Amurka da ta hanzarta soke wannan kuduri. In ba haka ba, tabbas kasar Sin za ta mayar da martani yadda ya kamata. (Tasallah Yuan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China