Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin za ta aiwatar da matakan hana biza ga Amurkawa dake da hannu kan batun yankin Hong Kong
2020-06-29 20:18:17        cri
Gwamnatin kasar Sin ta ce za ta kafa dokar hana takardun biza ga 'yan kasar Amurka dake da hannu kan batutuwan da suka shafi yankin musamman na Hong Kong.

Kakakin ma'aikatar harkokin wajen Sin Zhao Lijian, ya sanar da hakan a yau Litinin.

Kakakin ya yi wannan tsokaci ne a taron manema labarai da aka shirya domin mayar da martani kan matakin da kasar Amurka ta dauka na hana takardun biza ga wasu jami'an kasar Sin.

Har wa yau a taron manema labaran, mista Zhao Lijian ya ce, kasar Sin ta bukaci 'yan siyasar Amurka dake da ruwa da tsaki da su gaggauta gyara kurakuransu, su dena yiwa kasar Sin kalaman batanci, kana su guji aikata dukkan abubuwa da ka iya lalata dangantar dake tsakanin kasashen biyu da lahalta amincin dake tsakanin bangarorin biyu.

Zhao Lijian, ya kara da cewa, Afrika mahimman 'yan uwa ne ga kasar Sin dake da kyakkyawar nasaba iri daya. A wannan yanayi da ake ciki na barkewar annoba, Sin da Afrika suna aiki tare domin tinkarar annobar. Duk wani yunkuri na neman lalata alakar dake tsakanin Sin da Afrika saboda mummunan kudiri ba zai taba yin tasiri ba kuma ba zai yi nasara ba. (Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China