Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasar Sin ba ta cika baki ko yada bayanan karya don ta daga martabarta
2020-06-11 20:30:49        cri
Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Hua Chunying, ta bayyana a yau Alhamis cewa, baki dayan Sinawa sun sadaukar da kai har suka kai ga cimma nasarar yakar cutar COVID-19 cikin kankanin lokaci, Kuma kasar Sin ba ta taba cika baki ko yada bayanan karya domin ta daga martabarta a idon duniya ba.

Kalaman nata na zuwa ne, yayin da take mayar da martani kan rahotonnin baya-bayan nan da kungiyar tarayyar Turai ta yada, inda take zargin kasashen Rasha da Sin da yada bayanan karya.

Hua ta yi nuni da cewa, a fili yake cewa, duk wanda ya san gaskiya ya kuma fahimci hakikanin abin dake faruwa, ya san wanda ke kirkira da kuma yada labaran karya game da yaduwar cutar COVID-19, har ma kasashen duniya sun yi ta yada irin wadancan bayanan karya.

Ta ce, ya kamata EU ta fahimci ko akwai mutanen da ke yada bayanan karya a cikin kungiyar. A don haka, kasar Sin tana fatan bangaren EU zai yi aiki tare da kasar Sin da ma ragowar kasashen duniya, don kara amincewa da juna, da karfafa hadin aiki don ganin bayan wannan annoba, da sauran kwayar cutar siyasa bisa sanin ya kamata da neman sanin gaskiya daga shaidun da suka bayyana. (Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China