Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An gudanar da bikin kafa cibiyar nazarin tunanin diplomasiyya na Xi Jinping
2020-07-20 16:20:38        cri

A yau Litinin ne, aka gudanar da bikin kafa cibiyar nazarin tunanin diplomasiyya na Xi Jinping a nan birnin Beijing. Ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin ce ta kafa wannan cibiya, bisa dogaro da cibiyar nazarin harkokin kasa da kasa ta kasar, don yin amfani da albarkatun nazari na dukkan kasar Sin, wajen nazari da yin bayani da kuma gabatar da tunanin diplomasiyya na Xi Jinping a dukkan fannoni. Ta hakan za a yi amfani da rawar da tunanin ke takawa kan harkokin diplomasiyya wajen samar da gudummawar raya harkokin diplomasiyya mai hayalayyar musamman ta kasar Sin a sabon zamani da ake ciki.

Memban majalisar gudanarwar kasar Sin kuma ministan harkokin wajen kasar Wang Yi ne ya yi jawabi a gun bikin budewar, inda ya bayyana cewa, bayan gudanar da taron wakilan jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin karo na 18, babban sakataren kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin Xi Jinping ya gabatar da jerin sabbin tunani da ra'ayoyi da shawarwari masu alamar musamman ta Sin dake dacewa da yanayin bunkasuwar dan Adam a zamanin yanzu, kana an kafa tunanin diplomasiyya mai hayalayyar musamman ta kasar Sin a sabon zamani wato tunanin diplomasiyya na Xi Jinping, wanda ya bayyana hanyoyin da za a bi kan manufofin diplomasiyya na kasar Sin a nan gaba a sabon zamani. (Zainab)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China