2020-07-17 20:52:56 cri |
Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya jagoranci taron shugabanni game da ambaliyar ruwa da ta addabi wasu sassan kasar Sin. Shugaban wanda kuma shi ne babban sakataren kwamitin kolin JKS, ya jagoranci taron na yau Juma'a, domin tattauna matakan shawo kan ambaliyar, da kuma sauran ayyukan ba da agaji da ake gudanarwa.
Yayin taron na kwamitin kolin ofishin siyasa, karkashin kwamitin kolin JKS, shugaba Xi ya jaddada muhimmancin kare rayukan al'umma da dukiyoyin su, a matsayin abubuwan da suka fi komai muhimmanci. Ya kuma yi kira ga sassan masu ruwa da tsaki, da su kara azama wajen aiwatar da matakan dakile mummunan tasirin ambaliyar da ta auku, da ma fannin samar da agajin jin kai. (Saminu)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China