2020-07-16 13:43:47 cri |
A cikin wasikar, Xi ya nanata cewa, salon raya ci gaban tattalin arzikin kasar Sin mai dorewa bai canja ba, kuma ba zai taba canjawa ba. Ya ce kasarsa za ta ci gaba da zurfafa gyare-gyare a gida, da habaka bude kofa ga kasashen ketare, da samar da wani yanayin kasuwanci mai inganci ga kamfanonin gida da waje. Xi ya kuma jaddada cewa, kasarsa za ta nace ga bin hanyar neman bunkasuwa cikin lumana, da goyon-bayan dunkulewar tattalin arzikin duniya gu daya, ta yadda zai amfani kasashe daban-daban.
Kwamitin manyan shugabannin zartaswar kamfanonin kasa da kasa, wato Global CEO Council ya kunshi wasu manyan kamfanonin kasa da kasa 39, wadanda suka yi fice a bangarori daban-daban. A kwanakin baya, wasu shugabannin zartaswar kamfanonin 18 sun rubuta sako ga shugaba Xi Jinping, inda suka jinjina masa bisa shugabancin nagarin da ya yi, na ganin bayan cutar COVID-19 da farfado da harkokin yau da kullum a kasar Sin, lamarin da ya taka rawar a-zo-a-gani ga ayyukan yaki da annobar da tabbatar da bunkasuwar tattalin arzikin duniya yadda ya kamata.(Murtala Zhang)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China