Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Stephen Roach: Ya kamata Sin da Amurka su kara hadin kai don tinkarar kalubalen COVID-19
2020-07-09 09:58:56        cri
Asusun hadin kan Honkong, ya gabatar da lacca ta kafar Intanet a jiya Laraba, inda ya gayyaci masana da kwararru, don tattaunawa game da illar da COVID-19 take haifarwa ga bunkasuwar tattalin arzikin duniya.

Masani daga jami'ar Yale Stephen Roach ya yi kira a gun taro da cewa, kamata ya yi Sin da Amurka sun kara hadin kansu, don warware kalubalen cutar tare.

Bayan jawabinsa, Stephen Roach ya ce, duniya na fuskantar koma bayan tattalin arziki saboda barkewar wannan cuta, kuma kila za a fuskanci mawuyancin hali ta fuskar farfado da tattalin arzikin duniya.

Ban da wannan kuma, Stephen Roach ya yabawa matakai masu dacewa da Sin take dauka game da yakar cutar. Ya ce, ko da Amurka ba za ta iya kwaikwayon wadannan matakan da Sin take dauka ba, amma tana iya koyon dabarun kasar Sin, na amfani da kimiyya da fasaha a wannan yaki.

Daga nan sai ya jaddada cewa, hannu daya ba zai dauki jinka ba, don haka kamata ya yi, Sin da Amurka su yi hadin kai a fannin nazarin kimiyya da fasaha, da kiwon lafiya da dai sauran fannoni, haka kuma masana da masu ilimin kimiyya da fasaha na kasashen biyu, sun hada gwiwa wajen ba da gudunmawar fitar da allurar rigakafi cikin gaggawa.

Haka zalika, Stephen Roach ya bayyana cewa, bai kamata wasu 'yan siyasar Amurka su yi yunkurin bata sunan kasar Sin bisa muradun siyasa ba. A maimakon haka, dole ne su hada kai da kasar Sin, don cin moriya tare. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China