Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kenya ta gabatar da 'yar takarar babban jami'in hukumar WTO
2020-07-09 13:41:53        cri
Jiya Laraba, hukumar cinikayya ta duniya WTO ta sanar da cewa, kasar Kenya ta gabatar da ministar harkokin motsa jiki da al'adu ta kasarta Amina Mohammed a matsayin 'yar takarar babban jami'in hukumar.

Amina Mohammed ta taba zama zaunanniyar wakiliyar kasar Kenya dake WTO, da ministar harkokin waje da cinikin kasa da kasa ta kasar Kenya, kana ta taba zama shugabar majalisar zartaswar WTO, da shugabar taron ministocin hukumar na shekarar 2015 da aka yi a birnin Nairobi, fadar mulkin kasar Kenya. Kuma, ta taba halartar zaben babban jami'in hukumar na shekarar 2012.

A watan Mayu, babban jami'in hukumar WTO na yanzu Roberto Azevedo ya sanar da cewa, zai sauka daga mukaminsa a ranar 31 ga watan Agusta a hukumance, kafin shekara daya bisa wa'adin aikinsa. Kuma a ranar 8 ga watan Yuni, aka kaddamar da aikin zaben sabon babban jami'in hukumar a hukumance, kana ranar 8 ga watan Yuli ce rana ta karshe ta gabatar da 'yan takaran zaben. Kafin haka kuma, akwai kasashe guda biyar da suka gabatar da 'yan takaransu, wadanda suka hada da kasar Mexico da kasar Nijeriya, da kasar Masar, da kasar Moldova da kuma kasar Koriya ta Kudu. (Maryam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China