Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
WTO ta ce yawan cinikayyar kayayyaki a duniya zai ragu da kaso 18.5 a rubu'i na biyu na bana
2020-06-24 10:39:50        cri
Hukumar kula da cinikayya ta duniya WTO, ta ce yawan cinikayyar kayayyaki a duniya zai ragu da kaso 18.5 a rubu'i na biyu na bana

Cikin wata sanarwa da ta fitar, Darakta Janar na hukumar, Roberto Azevedo, ya ce raguwar cinikayya da ake gani yanzu, shi ne mafi girma a tarihi, kuma yana iya zama mafi muni. Amma duk da haka ana da kyakkyawar fata, yana mai cewa ba dan haka, yanayin ka iya fin haka muni.

A rahotanninta na farko, WTO ta yi hasashen cewa cinikayyar za ta ragu da kaso 13 zuwa 32 a bana saboda annobar COVID-19.

Hukumar ta bayyana cikin hasashen kididdigar cinikayya a duniya da ta yi cewa, bisa yanayin da ake ciki yanzu, ana bukatar cinikayyar ta karu da kaso 2.5 a kowanne rubu'i na sauran shekara, domin cimma mizanin hasashen da aka yi. Ta kara da cewa, matakan gaggawa da gwamnatoci suka dauka na tunkarar cutar, sun taimaka wajen rage tasirinta. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China