Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kotun daukaka kara ta WTO za ta dakatar da sauraron kararraki
2019-12-11 10:53:05        cri

Babban daraktan kungiyar cinikayya ta duniya WTO Roberto Azevedo, ya ce daga ranar Larabar nan, kotun kungiyar mai sauraron kararraki da ake daukakawa, za ta dakatar da sauraron sabbin kararraki. Mr. Azevedo ya bayyana hakan ne, yayin wani taron manema labarai da ya gudana a hedkwatar WTOn dake birnin Geneva.

Ya ce a yanzu haka, yana da kyau a jaddada cewa, hukuncin da WTO ta yanke ne kawai za a iya dogaro da shi. Kaza lika kasashe mambobin kungiyar za su ci gaba ne da aiwatar da kudurorin WTO, bisa manufofinsu na kare tattalin arziki, da martaba dokokin da aka amincewa, da burinsu na tabbatar da kyakkyawar alaka da abokansu na cinikayya.

Babban daraktan WTOn ya bayyana hakan ne ga 'yan jarida, bayan taro na yini biyu da mambobin majalissar kungiyar, wadanda suka gaza cimma daidaito game da sabunta mambobin kotun daukaka karar, sakamakon rashin amincewa daga tsagin Amurka.

Kotun dai ita ce ke aikin sauraron kararrakin da aka daukaka a kungiyar ta WTO, tana kuma da mambobi 7, kuma sai akwai a kalla 3 daga cikin su kafin sauraron duk wata kara da za a gabatar mata. To sai dai a hanlin yanzu, mamba daya ne kacal ya rage a kotun, don haka tun daga yau Laraba, kotun ba za ta iya sake sauraron wata kara da za a daukaka gaban ta ba. (Saminu Hassan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China