Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasashe 52 sun yi maraba da aiwatar da dokar tsaro a yankin HK
2020-07-01 10:02:31        cri

Kasashe 52 wadanda kasar Cuba ta yi magana a madadinsu jiya Talata, yayin taron hukumar kare hakkin dan-Adam ta MDD karo na 44, sun yi maraba da matakin majalisar wakilan jama'ar kasar Sin na sanya hannu kan dokar tsaro a yankin musamman na Hong Kong na kasar Sin.

Da yake karanta sanarwar hadin gwiwar, wakilin kasar Cuba a taron, ya bayyana cewa, ana saran yawan kasashen da za su sanya hannu kan sanarwar hadin gwiwar zai karu. Yana mai cewa, rashin tsoma baki a harkokin cikin gidan kasashe, wani muhimmin bangare ne dake cikin dokokin MDD da ma tushen alakar kasa da kasa.

Sanin kowa ne cewa, ikon majalisar dokoki kan batutuwan da suka shafi tsaro, ya rayaya ga kasar, don haka ba batu ne na kare hakkin dan-Adam ba, saboda haka wannan ba batu ne da hukumar za ta tattauna a kai ba.

Kasashen sun kuma yi imanin cewa, kowa ce kasa tana da 'yancin kare tsaron kasarta ta hanyar kafa dokoki da daukar matakan da suka dace kan wannan batu.

A saboda haka, sanarwar ta ce "muna maraba da shawarar da majalisar wakilan jama'ar kasar Sin ta yanke ta kafawa da kuma inganta matakan tsaro don kare yankin musamman na Hong Kong da ma tsaron kasa baki daya, da tabbatar da martaba tsarin nan na kasa daya, amma tsarin mulki iri biyu.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China